in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawa 3 sun samu raunuka sanadiyyar 'yan fashi a Afrika ta Kudu
2017-02-06 10:27:56 cri

Wani jami'in ofishin jakadancin kasar Sin a Afrika ta Kudu ya ce, wasu Sinawa 3 'yan yawon shakatawa sun samu raunuka a sakamakon 'yan fashi da suka afka musu a wani otel a kasar Afrika ta Kudu.

Iyalan su 3, wadanda suka fito daga lardin Guangxi na kudancin kasar Sin, sun gamu da wannan tsautsayi ne, a lokacin da suka isa wani otel dake birnin Johannesburg, da misalin karfe 10 na dare a ranar Asabar, bayan kammala hutunsu. Inda suke sa ran komawa gida a ranar Lahadi.

Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya ba da rahoton cewa, iyalan suna kokarin zama a otel din ne a lokacin da 'yan fashin suka yi musu dirar mikiya, suka kwace musu kayayyaki, kana suka harbi matar a kai, mijinta kuma a kirji da kafa, yayin da 'yarsu ta samu kananan raunuka.

Sai dai tuni barayin suka tsere da jakakkunan hannun iyalan, kuma an garzaya da su zuwa wani karamin asibiti domin kula da lafiyarsu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China