in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu ta shirya karbar bakuncin taron WEF
2017-05-03 10:10:36 cri

Mahukunatn kasar Afirka ta Kudu sun bayyana cewa, sun shirya tsaf, don karbar bakuncin taron dandalin tattalin arziki na duniya (WEF) da za a gudanar a birnin Durban.

Taron wanda zai gudana daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Mayun wannan shekara, ana sa ran zai samu halartar wakilai sama da 2,000 wadanda suka hada da shugabannin kasashe 21 da shugabannin 'yan kasuwa, da na kungiyoyin fararen hula da kafofin watsa labarai da na fasaha. Ana kuma fatan za su tattauna batutuwan da suka shafi ci gaba da sauran muhimman batutuwa dake shafar yanayin tattalin arzikin duniya da sauransu.

Birnin eThekwini wanda zai karbi bakuncin taron ya tabbatar a jiya Talata cewa, yanzu haka ya shirya karbar bakuncin wannan taro. An kuma rufe hanyoyi dake kusa da dandalin taron, kana an tanadi kayayyaki da cibiyoyin kiwon lafiya, da jami'an da za su daidaita cunkoson jama'a da na ababan hawa a lokacin taron.

Da ya ke karin haske game da fa'idar wannan taro, Philip Sithole mai rikon mukamin mataimakin shugaban birnin mai kula da harkokin raya tattalin arziki da tsare-tsare, ya ce babu shakka birnin zai ci gajiyar wannan taro.

Ita ma rundunar 'yan sandan kasar Afirka ta Kudu ta bayyana ta bakin kakakinta Birgediya Vishnu Naidoo cewa, a shirya ta ke ta kare rayuka da dukiyoyin mahalarta taro. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China