in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta gudanar da taron alhinin cika shekaru 23 da kisan kare dangi na aka yi a Rwanda
2017-04-08 13:06:49 cri
Tarrayyar Afrika AU, ta gudanar da taron tunawa da kisan kare dangi da aka yi a Rwanda wanda ke cika shekaru 23 a jiya Juma'a.

Taken Taron wanda aka yi a hedkwatar kungiyar dake birnin Addis Ababa na Habasha, tare da hadin gwiwar ofishin jakadancin Rwanda dake kasar, shi ne 'tunawa da kisan kare dangi na Rwanda - yaki da akidar kisan kare dangi - kara inganta nasarorinmu'

Tarayyar Afrika ta ce manufar taron ita ce, tunawa da rayukan da aka yi asararsu a Rwanda a shekarar 1994, da nuna goyon baya da kauna ga wadanda suka kubuta tare da kara inganta hadin kai, domin tabbatar da makamancin al'amarin ba zai kara faruwa a kasar Rwanda ba, ko wata kasa a Afrika ko duniya baki daya.

Da yake jawabi yayin taron, mataimakin shugaban kungiyar Thomas Kwasi Quartey, ya jadadda cewa, ana gudanar da taron ne duk shekara a ranar 7 ga watan Afrilu, domin tunawa da wandanda al'amarin ya rutsa da su, tare da sake sabonta kudurin al'ummar nahiyar Afika na kare 'yancin dan Adam. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China