Gwamnatin tsakiya ta kebe sama da yuan biliyan 86, wato sama da kashi 30.3 bisa 100 idan aka kwatanta da na shekarar bara. Kimanin yuan biliyan 54 ne aka ware wa hukumomin gudanarwa na larduna 28 a fadin kasar Sin.
A karshen shekarar da ta gabata, kasar Sin tana da adadin mutane miliyan 43 ne wadanda ke fama da kangin talauci a yankunan karkara.
Da ma dai gwamnatin Sin ta sha nanata aniyarta na tsamo al'ummar Sinawa mazauna karkara daga cikin kangin fatara, karkashin shirin yaki da talauci nan da shekarar 2020, domin gina tsarin al'umma mai matsakaiciyar wadata.
Tun lokacin da kasar Sin ta fara aiwatar da sauye-sauyen manufofinta da bude kofa kasashen duniya nan da shekaru kusan 40 da suka gabata, kawo yanzu Sinawa miliyan 700 ne suka yi ban kwana da matsanancin talauci, wanda ya kai adaddin kashi 70 na yawan mutanen da suka fita daga cikin kangin talauci a duniya a tsawon wannan lokaci. (Ahmad Fagam)