Nutsewar ta yau Alhamis ita ce karo na biyu a bana, inda ake sa ran zai dauke ta sa'o'i da ba za su gaza 10 ba.
Na'urar za ta dauko samfurin ruwan teku da duwatsu da wasu halittun ruwa tare da yin nazari da gwaji da daukar hotunan a can kusa da kasan tekun.
Masana kimiyya na kasar Sin na shirin nutsewa a sashen tekun na Mariana Trench har sau biyar.
Nutsewar ta farko ta gudanan ne a ranar Talata, inda wani dan jarida ma'aikacin kamfanin dillanci labarai na Xinhua ya bi tawagar masana kimiyya da suka nutse da mitoci 4,4811. (Fa'iza Mustapha)