Wani rahoton bincike game da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka da aka fitar wanda ma'aikatar ta fitar ya nuna cewa, tun shekarar 2005, kasar Sin take kokarin ganin ta inganta yadda ake musayar kudin kasar a kasuwannin musaya, kuma darajar RMB din ta inganta.
Ma'aikatar ta kuma yi nuni da cewa, ba a ambaci sashen kula da harkokin kasuwannin musayar kudade na babban bankin kasar a maganar rage darajar musayar RMB din ba.
Ta kara da cewa, matakan da kasar Sin ta dauka na inganta darajar musayar kudin kasar da daidaita darajar musayar kudin sun rage illar da hakan ka iya haifarwa kan yadda za a daidaita darajar musayar RMB da takarar rage darajar musaya kan manyan kudaden da ake amfani da su, matakin da zai amfanawa al'ummomin kasa da kasa ciki har da Amurka.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, kasar Sin ba za ta taba shiga gasar rage darajar musayar kudade ba. Gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakan tabbatar da cewa, darajar musayar RMB a kan dalar Amurka zai ci gaba da kasancewa a dukkan fannoni. (Ibrahim Yaya)