Ma'aikatan kimiyya da ke cikin jirgin sun kwashe tsawon sa'o'i kusan 9 a karkashin ruwa, inda suka gudanar da bincike tare da dauko samfuran abubuwa daban-daban, ban da haka, sun kuma dauki dimbin hotuna masu inganci.
Chen Xinhua, babban masanin kimiyya da ke cikin jirgin ya ce, samfuran duwatsu da aka dauka a yayin wannan nutsewa suna da muhimmiyar ma'ana ta bangaren nazarin kwarin Mariana, musamman bullarsa da kuma bunkasuwarsa. Sauran samfuran halittu da aka dauko daga kwarin za su taimaka ga binciken kasancewar nau'o'in halittu yadda halittun suke gudanar da rayuwarsa a karkashin ruwa mai zurfi. (Lubabatu)