Li Weisen, mataimakin daraktan gudanar da sha'anin safiyo, shata wurare, da tattara bayanai, ya bayyana cewa tsarin ya kushi tashoshi 2,700, da cibiyar tattara bayanai da kuma matakan larduna 30 na ajiye bayanai.
Tsarin yana da sauri wajen gudanar da aiki, yana da inganci wajen daukar taswirar wurare masu yawa, kuma zai dace da tsarin ragowar tauraron dan adam, kamar tsarin tauraron dan adam na BeiDou Navigation da na Global Position System wato GPS a takaice, inji Li.
A cewar hukumar gudanarwa, tsarin zai iya samar da yanayin sadarwa ga masu harkokin sufuri, da masu aikin ba da kulawar gaggawa ga marasa lafiya, da fannin gudanar da al'amurran mulki. (Ahmad Fagam)