Kasar Sin tana shirin harba wasu taurarin dan-Adam masu shawagi na Beidou guda 18 nan da shekarar 2018.
Shugaban kwamitin kula da tsarin shawagin tauraron dan-Adam na kasar Sin Wang Li ne ya bayyana hakan, lokacin da yake jawabi a taron shekara-shekara na cibiyar nazarin harkokin tauraron dan-Adam na kasar Sin karo na 8. Yana mai cewa, za a harba taurarin dan-Adan na Beidou 6 zuwa 8 cikin sararin samaniya a cikin watanni 6 na karshen wannan shekara.
Wang ya ce, tsarin tauraron dan-Adam na Beidou da kasar ta Sin ta ke shirin harbawa zai samar da hidima ga kasashen da shawarar ziri daya da hanya daya ta shafa.
Jami'in ya ce, nan da shekarar 2020, taurarin dan-Adam na Beidou da kasar Sin take fatan harbawa za su kasance cikamakin tsarin shawagin tauraron dan-Adam na duniya.(Ibrahim)