in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasar Sin sun jajantawa takwaransu na kasar Masar
2017-05-27 13:14:13 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon jaje ga takwaransa na kasar Masar Abdel-Fattah El-Sisi, inda ya nuna bakin cikinsa kan rasuwar mutanen da ba su san hawa ba su san sauka ba, sakamakon harin ta'addanci da aka kai jihar El Minya ta kasar Masar a jiya Juma'a, ya na mai jajantawa shugaba El-Sisi, da iyalan wadanda suka mutu, da mutanen da suka jikkata sakamakon harin.

Haka zalika, shugaban na kasar Sin ya ce kasarsa ba ta goyon bayan kowane irin aikin ta'addanci, don haka ya yi Allah wadai da wadanda suka kai wannan mummunan hari da kakkausan harshe.

Har ila yau, Shugaba Xi ya ce a ko da yaushe, kasar Sin ta na goyon bayan kasar Masar kan kokarin da take na kiyaye tsaro da dakile ta'addanci.

Shi ma a nasa bangaren, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya aike da sakon ta'aziyya ga takwaransa na kasar Sherif Ismail.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China