A cewar shugaban kasar Sin, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Habasha ta riga ta zama kan gaba a hadin gwiwar da ake yi tsakanin bangarorin Sin da Afirka. Don nuna muhimmancin huldar dake tsakanin kasashen 2, da matsayin da suka cimma a fannin amincewa da juna, shugaban kasar Sin ya ba da shawarar daga matsayin huldar dake tsakanin kasashen 2, zuwa irin abokantakar da ta shafi hadin gwiwa ta fuskar manyan tsare-tsare.
Shugaban ya kara da cewa, kasar Sin ta taya ma kasar Habasha murnar shiga cikin jerin mambobin bankin zuba jari ga kayayyakin more rayuwa na Asiya, kuma za ta ci gaba da goyon bayan kasar Habasha domin ta taka rawar hada nahiyar Afirka da sauran nahiyoyi bisa shawarar "ziri daya da hanya daya"
A nasa bangaren, firaministan kasar Habasha, Hailemariam Dessalegn, ya ce shawarar "ziri daya da hanya daya" tana da ma'ana mai zurfi ga duniya, kuma ta nuna hangen nesa da sanin ya kamata. Wannan shawara a cewar shugaban, za ta taimakawa hada yankuna daban daban na duniya, da karfafa hadin gwiwa a fannin cinikayya da zuba jari. Saboda haka, kasar Habasha ta yi kokarin halartar ayyukan hadin kai da ake yi karkarshin laimar shawarar "ziri daya da hanya daya".(Bello Wang)