Mr. Meng ya ce bisa la'akari da yanayi mai tsanani da ake ciki a fannin yaki da ta'addanci, kasar Sin na fatan ganin kafuwar wani tsarin hadin kai ta fuskar yakar ta'addanci wanda ke yaduwa cikin sauri ta hanyar yanar gizo ko Internet.
Mr. Meng ya yi wannan tsokaci ne yayin wani taron manyan kusoshi a fannin aikin tsaro wanda aka kira a kasar Rasha, ya ce a bisa tsarin hadin gwiwa ne za a kara hada karfi waje guda don samun kwanciyar hankali a duniya, da tabbatar da tsaron jama'ar kasashe daban daban, da yunkurin dakile ta'addanci.
Taron dai ya samun halartar wakilai na kasashe da kungiyoyi 95.(Bello Wang)