in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yaba da matakin kasar Sin game da hadin gwiwa a fannin tsaron Intanet
2017-03-03 10:39:07 cri
Kakakin MDD Stephane Dujarric ya bayyana cewa, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a hadin gwiwar tsaron yanzar gizo ta Intanet a duniya.

Mr. Dujarric ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis yayin taron manema labarai, yana mai cewa matakin farko da kasar Sin ta dauka game da tsaron yanar gizo labari ne mai dadin ji.

A ranar Larabar da ta gabata ce kasar ta Sin ta fitar da matakanta na hadin gwiwa game da tsaron yanar gizo. Wannan shi ne rahoto irinsa na farko da mahukuntan kasar Sin suka fitar game da yadda kasashen duniya za su hada gwiwa a fannin tsaron intanet.

Sabon rahoton ya jaddada muhimmanci ganin MDD ta kasance a kan gaba wajen yayata bukatar hadin gwiwar kasashen duniya a fannin tsaron yanar gizo.

Manufar wannan mataki na kasar Sin ita ce, gina al'ummar da za ta rika cin gajiyar yanar gizo ta hanyar zaman lafiya da mutunta 'yancin kasa da musayar da al'amuran da suka shafi harkokin mulki da cin moriyar juna. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China