Kafofin yada labarai na kasar Amurka a wannan rana sun ruwaito wani jami'in sashen kula da harkokin kasafin kudi na fadar White House yana cewa, Mr. Trump na shirin kara kashi 10 cikin 100 na kudin da za a kasaftawa fannin tsaro, wato kimanin dala biliyan 54, a yayin da za a rage kudin a wasu fannonin da ba su shafi harkokin tsaro ba, misali fannin samar da taimako ga kasashen waje. (Lubabatu)