in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Benin da Najeriya za su bunkasa hadin gwiwa a fannin tattalin arziki
2017-05-25 08:54:34 cri

Rahotanni daga Benin na cewa, a yau Alhamis ne ake sa ran ministan masana'antu, cinikayya da sana'o'in hannu na kasar Lazare Sehoueto zai jagoranci wata tawaga daga ma'aikatar kula da harkokin masana'antu da cinikayya ta kasar zuwa Abuja, babban birnin Najeriya don tattauna hanyoyin bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin sassan biyu.

Wannan wani bangare ne na matakan da gwamnatin Benin ta bullo da su da nufin karfafa hadin gwiwar diflomasiya tsakanin kasashen biyu. A lokacin wannan ziyara, ana sa ran Lazare zai halarci wani taron bunkasa musayar harkokin cinikayya a Najeriya, don gano damammakin tattalin arziki wadanda za su taimakawa kasar ta Benin samun ci gaba mai dorewa.

Ana kuma sa ran ita ma tawagar kasar ta Benin za ta yi amfani da wannan dama wajen nunawa masu ruwa da tsaki a harkar tattalin arzikin Najeriyar, da ma jami'an siyasar kasar tarin damammakin da kasar ta Benin ke da su a fannin harkokinn kasuwanci.

Bayanai na nuna cewa, tun a shekarar 1970 ne dai hulda tsakanin kasashen biyu ta ke bunkasa, sakamakon hadin gwiwar taimakon juna gami da yarjeniyoyin a fannonin siyasa da tattalin arziki da tsare-tsare, da kimiya, da tsaro da kuma al'adu da sassan biyu suka kulla a tsakaninsu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China