in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Benin ta yi maraba da tawagar likitocin Sin ta 21
2016-11-03 13:30:14 cri

Jamhuriyar Benin ta yi maraba da tawagar jami'an kiwon lafiya ta 21 da kasar Sin ta tura zuwa kasar, kuma tuni suka isa Cotonou, babban birnin kasar, likitocin za su gudanar da muhimman ayyukan kiwon lafiya a kasar.

Tawagar ta kunshi kwararrun likitoci 27, wadanda suka isa kasar tun a ranar Talata. Kimanin watanni 12 za su shafe suna gudanar da ayyuka a asibitoci 3 a biranen kasar wadanda suka hada da Lokossa da Natitingou.

Wata majiya daga ma'aikatar lafiya ta jamhuriyar Benin ta bayyana cewa, kasar tana kwadayin samun karin wasu jami'an kiwon lafiyar daga kasar Sin, wadanda za su gudanar da ayyukan tiyatar idanu, a wani mataki na magance matsaloli ga jama'a dake fama da lalurar ciwon ido a kasar.

Jamhuriyar Benin, tana burin ci gaba da karfafa dangantakarta da kasar Sin a fannin kiwon lafiya, musamman a bangaren magungunan gargajiya.

Sama da jami'an kiwon lafiyar kasar Sin 400 ne, suka gudanar da ayyuka dabam dabam a jamhuriyar Benin, karkashin shirin hadin gwiwar Sin da jamhuriyar Benin, wadanda suka ba da gagarumar gudunmowa ga sha'anin kiwon lafiyar jama'ar jamhuriyar Benin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China