in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 4,000 da Boko Haram ta yi garkuwa su ne suka samu 'yanci
2017-05-19 10:07:51 cri

Ministan tsaron Nijeriya Mansur Dan-Ali, ya ce kawo yanzu, jami'an tsaro sun ceto a kalla mutane 4,000 da ke hannun kungiyar Boko Haram.

Da yake jawabi yayin wani taro a birnin Jos, Mansur Dan-Ali ya ce, daga cikin wadanda aka ceto har da 'yan mata 106 na sakadaren garin Chibok dake jihar Borno a arewa maso gabashin kasar, da kungiyar ta sace a shekarar 2014.

Ya ce, galibin wadanda suka samu 'yancin mata ne da kananan yara.

A cewar Dan-Ali, jajircewar kawancen rundunonin tsaro, ya yi nasarar karya lagon mayakan Boko Haram, al'amarin da ya sa sake hadewar kungiyar tare da shirya kai hare-hare a yankin na arewa maso gabashin kasar, zai yi matukar wahala.

Tun daga shekarar 2009, kungiyar Boko Haram ta yi sanadin mutuwar dubban mutane, tare da raba mutane miliyan 2.3 da matsugunansu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China