in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kusa a jam'iyya mai mulkin Najeriya ya gargadi masu yunkurin juyin mulki
2017-05-23 09:36:11 cri

Uban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ya bayyana cewa, babu wata sauran dama ta kitsa juyin mulki a kasar.

Bola Tinubu, kuma tsohon gwamnan jihar Legas, jigo ne a jam'iyyar APC mai mulki, ya yi wannan gargadi ne a lokacin zama na musamman na majalisar dokokin jihar Legas domin bikin cikar shekaru 50 na kafuwar jihar.

Ya bayyana Legas, cibiyar kasuwancin kasar cewa, za ta iya kare duk wani yunkuri na kifar da tsarin demokaradiyya, kuma haka dukkan sauran sassan kasar ba za su laminci rusa demokaradiyyar ba.

Idan za a iya tunawa, rundunar sojin Najeriya ta gargadi manya da kananan jami'anta da su guji shiga harkokin siyasa.

Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriyar Sani Usman, shi ne ya sanar da hakan a wata sanarwar, inda shugaban rundunar sojin Najeriyar Tukur Buratai ya bayyana cewa, wasu 'yan siyasa suna tunkarar jami'an sojin kasar saboda wasu dalilai irin na siyasa wanda ba'a bayyana su ba.

A cewar wannan sanarwa, Buratai, ya shawarci jami'an sojin dake da sha'awar shiga siyasa da su yi murabus daga aikin sojin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China