in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayern kasha euro miliyan 100 don cinikin yan wasa, inji Hoeness
2017-05-24 19:54:37 cri
Bayan rashin nasara a wannan kakar wasan inda ta samu matsayi guda daya tak, kungiyar wasan kwallon kafa ta Bayern Munich ta sanar da cewa, tana shirin zuba jarin kudade masu yawa don mallakar sabbin yan wasa. Uli Hoeness, shugaban 2017 German champion, ya sanar da cewa kulob din zai yi garambawul game da shirinsa na zuba jari. Sama da zunzurutun kudi euro miliyan 100 ne kulob din zai kebe domin tada komadar kungiyar wasan domin ta samu damar tunkarar manyan kungiyoyin wasan kwallon kafa na turai kamar su Real, Juventus Turin da kuma FC Barcelona.

Hoeness ya tabbatar da cewa lambar yabo daya kwal ba zata iya gamsar da kungiyar wasan game da burin da take dashi ba. Shugaban kungiyar mai shekaru 65 yana sane da cewa kulob din zai iya zarce matsayin da yake dashi a baya, "domin mu samar da kyakkyawar kungiyar wasa ya zama tilas mu sayo manya zakarun yan wasa daga kungiyoyin wasan kwallon kafa na duniya."

Bayan ritayar da kaftin din kungiyar wasan Philipp Lahm, yayi daga aiki, wanda keeper Manuel Neuer da dan wasan tsakiya na Spaniya Xabi Alonso zasu maye gurbinsa, zai yi matukar wahala ga Bayern ta iya samun inganci irin guda.

Bayan fitar dashi daga wasan Champions League tun a farkon wasan na kusa da karshe daga Real Madrid da kuma kofin German Cup a wasan kusa dana karshe daga Borussia Dortmund, Hoeness ya fada cewa kulob din za'a tilastashi ya biya wasu kudade wanda zai yi wuya a halin yanzu amma wannan abune da aka saba dashi a yayin kasuwar musaya. Babban muhimmin abu shine samar da gamayyar kwararru kuma matasa a babban mataki, Hoeness shine ya jaddada hakan.

Baya ga Niklas Suele da Sebastian Rudy (TSG Hoffenheim) ana rade radi game da fitattun yan wasan na kasa da kasa kamar su Alexis Sanchez (Arsenal) da Marco Verratti (Paris St. Germain) da matashin dan wasan tsakiya na FC Schalke, Leon Goretzka sune burin Bayern. "Idan har Bayern tana son yan wasa dole ne mu zuba kudaden da suka dace," Hoeness ya fadi hakan.

Karin zuba jari zai kara snya tsammani idan aka zo maganar babban kociya Carlo Ancelotti. Kociyan mai shekaru 57 dan asalin kasar Italiya, ana saran kakar wasa ta biyu itace damarsa ta karshe da zai iya gamsar da muradun da kungiyar wasan ta Bavarian take dashi. A yanzu, manyan jami'in dake jagorar kulob din Hoeness da babban jami'in kungiyar wasan Karl-Heinz Rummenigge suna da burin karbe aikin kociyan domin amfani da wani salon a zawarcin kwararrun yan wasa kamar su Joshua Kimmich ko Renato Sanches.

Wadan da ke ciki suna fadin cewa ya kamata Ancelotti ya nemi mataimaki wanda ya dace domin cike gibin da Paul Clement ya bari bayan tafiyarsa kuma ya kamata ya nemo Karin fitattun yan wasa matasa. Rashin lokacin wasa, gami da tsarin bada horo da kociyan ke amfani dashi shine wannan bai taimaka ba wajen horas da matasan yan wasan wasu ma na ganin hakan ne ya haddasa rashin samun sakamako mai kyau lamarin da ya sa kungiyar ta kwashi kashinta a hannun German international Kimmich, da Sanches da Kingsley Coman. Manyan jami'an Bayernsuna son kare Kimmich da sauransu domin su samu nasara a shekara ta gaba.

Bayyanan nan abune Bayern tana sa ido a kan Julian Nagelsmann,ma shekaru 29 na TSG Hoffenheim, wanda ya ganma kakar wasanni cikin nasara zagayen teburi na hudu. Ana yada jita jita cewa hukumar gudanarwar Bayerntana saran Ancelotti zai cigaba da zama da kungiyar wasan zuwa Karin shekara gudadaga nan sai ya tafi idan yana son canza kungiya.

Kungiyar wasan a kwanan nan ta sake bude wata cibiyar matasa. Euro miliyan 70 ta zuba jariusu kuma Hoeness yana saran samun kyakkyawan sakamako nan da yan shekaru masu zuwa. Tun bayan David Alaba, babu wani matashi da ya bugawa kungiyar wasa inji Hoeness. Kungiyar wasan tana son inganta harkokinta a nan gaba,

A cewar Hoeness, Bayern ta dukufa domin neman mafita nan da yan watanni masu zuwa. Dukkansu Lahm da Max Eberl, manajan darakta na league suna adawa da Borussia Moenchengladbach, sun bayyana alamar barin aikinsu da nufin ko hakan zai iya yin tasiri kan Hoeness .(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China