in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga CFA da ta binciki batun dukan jami'in kungiyar kwallon kafar Guizhou
2017-05-11 12:01:02 cri
Masu sha'awar wasan kwallon kafa, da masu ruwa da tsaki a nan kasar Sin, sun yi kira ga hukumar wasan kwallon kafar kasar CFA, da ta gudanar da bincike game da zargin da ake yiwa dan wasan Shanghai SIPG Hulk, na dukan jami'in kulaf din Guizhou.

A ranar asabar din karshen makon jiya ne, yayin da Shanghai SIPG ta doke kungiyar ta Guizhou da ci 3 da nema, kocin Guizhou Li Bing, ya yi zargin cewa Hulk dan asalin kasar Brazil, ya doki maitaimakin sa yayin da suke fita daga filin wasa. Ko da yake tuni kungiyar ta Shanghai SIPG ta karyata wannan zargi, tana mai bukatar mahukuntan Guizhou, da su gaggauta janye zargin da a cewar su ba shi da tushe bare makama.

Gabanin hakan dai an ce kociyan kungiyoyin 2, sun yi tankiya a yayin wasan na firimiyar kasar Sin. Daga bisani kuma Hulk ya shiga batun, inda ya bi mataimakin mai horas da kungiyar Guizhou hanyar fita filin wasan, lokacin da aka tafi hutun rabin lokaci ya lakada masu duka.

Da yake korafi game da hakan, koci Li Bing, ya ce suna fatan 'yan wasan ketare dake zuwa kasar Sin, baya ga daga marabar kwallon kasar, a hannu guda kuma za su zamo abun misali wajen nuna da'a da sanin ya kamata, maimakon nuna halin rashin dattaku. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China