Leo Messi ne ya fara saka kwallo a ragar Espanyol minti 8 da take wasa, sai kwallo Luis Suarez a minti na 52, da wata kwallon a minti na 60. Har wa yau Messi ya sake saka kwallo a ragar Espanyol kafin kuma Neymar ya kara kwallo ta biyar.
Yanzu haka dai Barcelona na bukatar lashe wasanta na gaba da Granada cikin mako mai zuwa, domin ta tabbatar da nasarar daukar kofin na La Liga, sai dai a daya hannu Real Madrid na ci gaba da dagewa domin ganin ta dauki kofin ita ma, inda ta samu nasarar wasan ta da Valecia da ci 3 da 2.
Cristiano Ronaldo ne ya ciwa Real Madrid kwallaye 2, kana Karim Benzema ya jefawa kungiyar kwallo ta 3. A daya bangaren 'yan wasan Valencia Rodrigo da Andre Gomes ne suka ciwa kulaf din su kwallo biyu a wasan.(Saminu Alhassan)