in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan kallo sun baiwa hamata iska a filin wasa a Brazil
2017-05-11 12:02:07 cri
A kalla mutane biyu ne aka tabbatar da jikkatar su, bayan da sassan 'yan kallo na kulaflikan Clube de Regatas da Centro Sportivo Alagoano suka baiwa hamata iska, ana daf da tashi daga wasan su na ranar Lahadi da suka buga a Maceio.

An dai tashi wasan ne Clube de Regatas Brasil na da kwallo daya, Centro Sportivo Alagoano kuma na nema. Wani mai magana da yawun kungiyar

Clube de Regatas ya ce an lakadawa wani magoyin bayan kungiyar su dukan kawo wuka, ta yadda ba shi da tabbashin ko mutumin zai rayu. Ya ce akwai kuma wani mutum guda wanda ya jikkata.

Sai dai a nasa bangare wanda ya ciwa kungiyar Clube de Regatas Brasil kwallo wato Neto Baiano, ya ce sam bai dace a maida wasan kwallo tamkar wani yaki ba, ya ce wasa hanya ce ta nishadantarwa ba wai kunna wutar rikici ba.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China