Dan wasan mai shekaru 56 a duniya, ya bayyana amincewarsa da wannan aiki da aka bashi kamar yadda ya wallafa a cikin shafin sada zumunta na Facebook a jiya Lahadi.
Maradona yace yana son ya tabbatarwa duniya cewa a yanzu shine sabon kociyan Al-Fujairah SC.
Dan wasan wanda ya taba yin nasarar daukar kofin kwallon kafa na duniya a shekarar 1986, ya samu aikin kociyan ne a karon farko, tun bayan da aka koreshi daga mukamin manajan kulub din na UAE bangaren Al Wasl a shekarar 2012.
Bugu da kari, rahotanni da ake bazawa a kafafaen yada labaran kasar Argentine na nuni da cewa, Edgardo Bauza shine zai ja akalar babbar kungiyar wasan kwallon kafa ta UAE, kasa da wata guda bayan da ya rasa aikinsa na kociyan kasar Argentina.
Mahdi Ali, shine yayi murabus daga matsayin kociyan na UAE a watan Maris bayan shafe shekaru 5 yana jan ragamar kungiyar.(Ahmad Fagam)