Wasan Marathon da ya gudana a Beijing
A kwanakin baya, an shirya wata gasar gudun yada kanin wani a nan birnin Beijing, wadda ta kasance irin mai rabin zango. Wato 'yan wasan da suka halarci wasan ba su bukatar gudun wani cikakken zango na Marathon na kilomita 42 da wani abu ba, maimakon haka sun yi gudun rabin tsawon zangon, wato kilomita 21 da wani bu.
A wajen wasan akwai mutane fiye da dubu 20, wadanda suka zo daga kasashe da yankuna 23, suka halarci wasan na gudu. A karshe wani dan wasan kasar Kenya da wata 'yar wasa ta kasar Tanzaniya sun lashe lambobin zinariya na rukunin maza da na mata, yayin da 'yan wasan kasar Sin suka lashe dukkan lambobin azurfa, da na tagulla.
Wannan gasa ita ce wata gagarumar gasar da ake gudanar da ita a duk shekara, tun daga shekarar 2016. Kafin haka, a kan shirya gasar gudun tsawon mita dubu 10 a nan birnin Beijing a lokacin bazara, maimakon wata gasar rabin zangon Marathon, wadda ta bukaci a yi gudun tsawon mita 21097.5. Sa'an nan ban da gasar na rabin zango, akwai gasar cikakken zango na gudun yada kanin wani da ake gudanarwa a nan birnin Beijing, wadda aka fara gudanar da ita a kowace shekara tun daga shekarar 1981. Sai dai waccan gasa a kan gudanar da ita a lokacin kaka, wato a watan Satumba zuwa na Oktoba a nan birnin Beijing. Duk lokacin da ake gudanar da gasar, a kan samu 'yan wasa na kasashe daban daban da suka zo domin halartar gasar gudun. Ban da su kwararrun 'yan wasa, sauran jama'a masu sha'awar wasan gudu ma su kan halarci gasar, wasu har sun yi gudu tare da iyalansu, inda aka mai da gasar ta zama wani biki mai armashi matuka. Ta haka, ana iya ganin yadda wasan gudun yada kanin wani yake samun karbuwa a nan kasar Sin.
Amfanin wasan gudun yada kanin wani
Duk wani irin wasan motsa jiki, da farko dai, yana tare da amfani ga gina jiki da kiyaye lafiya. Sa'an nan game da wasan gudu, masana sun riga sun tabbatar da amfaninsa ga kara karfin huhu da zuciyar mutum. Haka kuma yadda aka dade ana gudu zai taimaka ga rage kiba, wadda ta kan haddasa cututtuka daban daban masu alaka da zuciya da hanyar jini.
Haka zalika, idan mun dubi tsarin da ake bi wajen gudanar da wasan Marathon, za mu ga cewa ya kasance wani wasa ne na daukacin jama'a masu son wasan gudu. Domin ba a gudanar da wasan gudun yada kanin wani cikin wani filin wasa dalilin zangonsa mai tsawo. Duk lokacin da ake gudanar da gudun Marathon, a kan shata layin hanya na musamman tare da rufe wasu hanyoyi motoci, domin samar da isashen fili ga dubun-dubatar 'yan wasa masu halatar gasar. Ta wannan hanya, a kan mai da gasar ta zama wani gagarumin biki na jama'a masu sha'awar wasan gudu, inda wasunsu duk da cewa ba za su kammala cikakken zango na kilomita 42 da wani abu ba, amma su ma sun samu damar gwada fasahar su a gasar rabin zango, ko kuma ta zangon kilomita 5, da dai sauransu, tare da karfafa kaunarsu game da wasa na gudu.
A wata gasar gudun yada kanin wani da ya gudana a birnin Boston na kasar Amurka a kwanakin baya, wata mace mai suna Kathrine Switzer, wadda shekarunta sun kai 70, ita ma ta halarci gasar, tare da kammala gudu na cikakken zangon gasar. Ka ga idan ya kasance gasar wani wasa na daban, ba zai yiwu ba a yarda da wata tsohuwa mai shekaru 70 a duniya ta halarci gasa ba. Amma a wajen wasan gudun yada kanin wani, mutane suna da cikakken 'yanci wajen halartar wasan, illa dai an yi maka binciken lafiyar jiki, kuma an ga babu matsala ga jikinka.
Ban da wannan kuma, a ganina amfanin wasan Marathon ya hada da taimakawa 'yan wasan kasashen Afirka samun karin lambobin zinariya a gasannin gudun Marathon na kasashe daban daban, ta la'akari da cikakkiyar kwarewar da suke da ita a fannin gudun zango mai nisa.
Shiga gasar wasan gudun yada kanin wani na bukatar da karfin jiki da jurewa sosai, ta la'akari da nisan gudun da za a yi, don haka ko da wani kwararren dan wasan gudu ne, bai iya shiga wata gasar nan take, ba tare da shiga horo cikin wani dogon lokaci ba.
Horon da ake yi domin halartar gasar Marathon ya shafi gudu zuwa wani wuri mai nisa a kowace rana. Idan ba kwararrun 'yan wasa ba, su kan yi gudun tsawon kilomita 32 a mako guda, sa'an nan yayin share fagen gasar Marathon, za a iya kara yin gudu zuwa kilomita 64 a kowace mako.
Idan kwararrun 'yan wasa ne, to, za su iya kara bisa wannan matsayi don neman sanya jikin mutum ya kara zama mai jurewa ga wahalar gudu.
Yawancin fitattun 'yan wasan gudu maza su kan yi gudun fiye da tsawon kilomita 160 a kowace mako.
Za a dinga shiga irin wannan horo ne a kalla wasu watanni 5 zuwa 6 kafin farawar gasar, inda a kan kara nisan gudu sannu a hankali. Game da mutanen da suka fara shiga wasan gudun fanfalaki nan ba da dadewa ba, an ba su shawarar cewa su fara shiga horo a kalla wasu watanni 4 kafin gasar, sa'an nan yayin horo ya yi gudu a kwanaki 4 cikin mako guda, ya kuma yi hutu a sauran kwanaki 3.
Fasahar daidaita jiki bayan shiga gasar Marathon
Bayan da an kammala wata gasar wasan gudun yada kanin wani, tilas ne jikinsa zai gaji sosai. Kuma wahalar gudu mai tsanani ta kan haddasa sauyin yanayi ga kayayyakin ciki, da jijiyar mutum, don haka ana bukatar daukar wasu matakai don daidaita yanayin da jikin mutum ke ciki don magance illa ga lafiyar jiki. Matakan da a kan dauka sun hada da tausar wasu sassan jiki, da kara motsa jiki sannu a hankali, da cin abincin da suka kunshi sukari da sauran abubuwa masu gina jiki don taimakawa samun daidaitar yanayin jiki. Haka kuma an ce za a iya sanya kafafuwan mutum cikin ruwa mai sanyi har wasu tsawon mintuna 20, don sanya karin jini cikin kafafuwan, lamarin da zai iya saukaka ciwonsu.(Bello Wang)