Indongo ya kwabde shararren dan wasan danben duniya (WBA), Ricky Burns a lokacin da suka dambata a wasan danben na kasa da kasa wato (IBF) da kuma sashen WBA.
Dan kasar ta Namibiya, wanda ya samu lambar yabo ta IBF da kuma ta (IBO), wanda ya lashe a watan Disambar 2016 bayan yayiwa abokin karawarsa dan kasar Rasha Eduard Troyanovsky kwab daya a Moscow, shine wanda ya kankane wasan a zagaye na 12.
Indongo ya nunawa Burns aniyarsa ta neman yin galaba a wasan ne tun a tirmin farko na wasan, tun bayan da ya mayar dashi baya a lokacin karawar.
Burns yayi iyakar kokarinsa wajen mayar da martani a zagaye na 7 ta hanyar kaddamar da wasu zafafan hare hare amma kaddara ta riga fata domin kuwa gogan naka Indongo ya kwabshi a gaban dandazon magoya bayansa, a lokacin da ya gwabje mista Burns.
Dukkannin alkalan wasan 3, sun baiwa jarumin Indongo nasara, da 120-108, 118-110 and 116-112, da wannan nasara, jarumin ya zama dan kasar Namibiya na farko daya samu lambar yado ta duniya har sau uku a lokaci guda.
Da yake zantawa da kafar yada labarai ta Sky Sports bayan fafatawar, Indongo, ya bayyana cewar yana matukar farin ciki saboda samun lambobin yabon a lokaci guda, kuma kwazon da ya nuna saboda kasar Namibiya ne da kuma nahiyar Afrika.
Indongo ya zama gagara badau ne cikin wasanni 22 da aka fafata, kuma ya lashe dukkan zagayen wasannin damben 22, gwarzon dan damben yana da shekaru 34 a duniya.(Ahmad Fagam)