in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Mauritania zai gudanar da ziyarar aiki a nan kasar Sin
2015-09-07 18:40:53 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei, ya ce shugaban kasar Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz, zai gudanar da ziyarar aiki a nan kasar Sin, tsakanin ranekun 9 zuwa 16 ga watan nan na Satumba, bisa gayyatar da shugaba Xi Jinping ya yi masa.

Mr. Hong Lei wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labaru da ya gudana a Litinin din nan, ya kara da cewa yayin ziyarar ta shugaba Abdel Aziz, zai halarci bikin bude taron baje kolin hajojin kasar Sin da kasashen Larabawa wanda zai gudana a birnin Yinchuan, fadar mulkin yankin Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kansa, wanda ke Arewa maso Yammacin kasar Sin, baje kolin da za a gudanar tsakanin ranekun 10 zuwa 13 ga watan nan. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China