in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta kai ziyara kasar Mauritania
2016-12-05 10:55:16 cri
Bisa goron gayyatar da majalisar dokokin kasar Mauritania ta ba su, tawagar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da ke karkashin jagorancin mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar Qiangba Puncog ta kai ziyara kasar Mauritania daga ranar 2 zuwa 4 ga wata. A lokacin ziyarar, Qiangba Puncog ya yi shawarwari tare da shugaban majalisar dokokin kasar Mohamed Ould Boilil, sa'an nan ya kuma gana da shugaban majalisar dattawan kasar Mohamed Hacen Ould Hadj da kuma firaministan kasar Yahya Ould Hdmyn.

Qiangba Puncog ya bayyana cewa, Sin tana son hada kai tare da Mauritania wajen tabbatar da daidaiton da shugabannin kasashen biyu suka cimma tare da gudanar da mu'amala da tattaunawa a tsakanin majalisun dokokin kasashen biyu, don kara daukaka huldar kasashen biyu.

A nata bangare, Mauritania ta nuna yabo kan huldar da ke tsakanin kasashen biyu, kuma za ta ci gaba da nuna tsayayyen goyon baya ga kasar Sin kan batutuwan da ke shafar moriyarta da kuma jawo hankalinta, sa'an nan za ta ci gaba da zurfafa hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu ta fannoni daban daban, domin kawo alheri ga al'ummar kasashen biyu. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China