Wadannan likitoci Sinawa suna cikin tawagar masu aikin likitanci da kasar Sin ta tura ma kasar Mauritania a karo na 31, wadanda suka kammala wa'adin aikinsu da kuma za su dawo kasar Sin. Dalilin haka ne, aka shirya bikin domin yaba musu kan kokarin da suka yi na raya aikin likitanci a kasar Mauritania, da kara dankon zumuncin dake tsakanin kasashen 2.
Wasu manyan jami'an da suka hada da Boubacar Kan, ministan kiwon lafiya na kasar Mauritania, da Wu Dong, jakadan kasar Sin dake Mauritania, sun halarci bikin ba da lambobin yabo din, inda minista Boubacar Kan, a madadin shugaban kasarsa Mohamed Ould Abdel Aziz, ya mika takardun shaidar yabo ga likitocin kasar Sin, tare da nuna musu godiya kan gudunmowar da suka bayar a fannonin raya aikin jinya a kasar, da tabbatar da lafiyar jikin jama'ar kasar.(Bello Wang)