in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta cimma nasarar hakar "combustible ice" daga yankin teku
2017-05-19 11:23:59 cri
A ranar 18 ga wata, kasar Sin ta cimma nasarar gwajin hakar sabon nau'in iskar gas ta "combustible ice" daga yankin teku, kuma wannan shi ne karo na farko da kasar ta cimma nasarar wannan gwaji, lamarin da zai yi da tasiri matuka ga fannin sarrafa makamashi a nan gaba.

Haka kuma, ko wane ma'aunin cubic meter na sabon nau'in iskar gas din yana daidai da cubic meter na iskar gas wanda aka saba amfani da shi ta fuskar auki sau 164, lamarin da ya nuna cewa, ba kawai ya fi man fetur da kwal tasiri wajen samar da makamashi ba ne, yana kuma da fifiko ta fuskar kiyaye muhalli kwarai da gaske.

Bugu da kari, shugaban cibiyar ba da umurni kan wannan gwaji Ye Jianliang ya bayyana cewa, a halin yanzu, kasashen duniya suna daukar "combustible ice" a matsayin makamashin da zai maye gurbin man fetur da iskar gas, wanda zai kuma ba da gudummawa kan tsaron makamashi da bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China