in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci sake fasalin tattalin arzikin Afrika ta hanyar bunkasa masana'antu
2017-05-19 10:55:10 cri

Hukumar kula da tattalin arzikin nahiyar Afrika ta MDD (ECA) ta jadadda cewa, dole ne a yi wa tattalin arziki nahiyar garambawul a fannin masana'antu domin samun dawwamammiyar ci gaba na bai daya.

Mukkadashin sakataren zartarwa na hukumar ECA Abdalla Hamdok, ya ce, cikin shekaru 6 da suka gabata, ECA ta mai da hankali wajen taimakawa bunkasar masana'antu a Afrika, inda nahiyar ke da damar kawar da talauci da rashin daidaito da aikin yi ta hanyar bunkasa ayyukan masana'antu.

Abdalla Hamdok ya bayyana haka ne a jiya, yayin bude taron yini biyu, kan hanyoyin samar da dawwamamiyar ci gaba a nahiyar Afrika, mai taken 'tabbatar da samun ci gaba na bai daya mai dorewa"

Mukaddashin sakataren ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ci gaban da nahiyar ta samu cikin shekarun da suka gabata, bai yi wani tasiri na a zo a gani ba, wajen rage talauci da rashin aikin yi, yana mai jadadda bukatar inganta masana'antu.

Ya ce, kamata ya yi a yi koyi da kasashen da suka ci gaba kamar Sin, wadda ta magance talauci ta hanyar ayyukan masana'antu.

Har ila yau, ya ce, cinikayya na taka muhimmiyar rawa wajen habakar tattalin arzikin Afrika, kuma ayyukan masana'antu na da damar bunkasa harkokin cinikayya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China