in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UN-HABITAT ta yi kiran Afrika da ta bude bangarenta na ayyukan kudi
2015-07-10 10:22:12 cri

A ranar jiya Alhamis ne, hukumar shirin gidaje ta majalisar dinkin duniya UN-HABITAT ta yi kira ga kasashen Afrika da su saki bangarensu na ayyukan kudi domin kara janyo karin jari.

Masanin tattalin arzikin birane na hukumar, Marco Kamiya, ya bayyana cewa, bangaren ayyukan kudi yana da karfin kasancewa wani ginshikin bunkasa tattalin arzikin Afrika.

A cikin kasashe masu karfin tattalin arziki, bangaren ayyukan kudi na taimakawa fiye da kashi 70 cikin 100 na damammakin samar da ayyukan yi, idan aka kwatanta da na yakin kasashen Afrika da ke kudu da hamadar Sahara, inda yake wakiltar kashi 40 cikin 100 kawai, in ji mista Kamiya a yayin bikin kaddamar da rahoton taron MDD kan kasuwanci da ci gaba a birnin Nairobi.

Kwararren na tattalin arziki ya yi kiran nahiyar Afrika da ta kafa karin hanyoyin hada kai tsakanin kamfanoni da ayyukan kudi, tare da kara cewa, har yanzu akwai muhimman abubuwan sanya ido na kasuwancin ayyukan kudi a nahiyar Afrika. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China