in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kasashen Asiya da su goyi bayan kokarin Afirka na samun wakilci a kwamitin tsaron MDD
2015-04-24 10:46:44 cri

Shugaba Ernest Bai Koroma na Saliyo ya yi kira ga kasashen Asiya da su goyi bayan kokarin Afirka na samun wakilci a kwamitin tsaro na MDD.

Shugaba Koroma ya yi wannan kiran ne a taron kolin Asiya da Afirka da ya gudana a Jakarta na kasar Indonesia.

Ya ce, duk da cewa nahiyar Afirka na da kasashe 54, amma har yanzu ba ta da wakilci a kwamitin tsaro na MDD, ganin cewa, sama da kashi 70 cikin 100 na abubuwan da ake tattaunawa batutuwa ne da suka shafi nahiyar ta Afirka, don haka wannan ba adalci ba ne, kuma wajibi ne a duba wannan batu da idon basira.

Kasashen Sin, Faransa, Rasha, Burtaniya da Amurka su ne mambobin din-din-din a kwamitin tsaron na MDD.

Bayanai na nuna cewa, galibin kasashen Afirka ba su samu 'yancin ba a lokacin da aka kafa MDD a shekara 1945.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China