in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararrun Kenya sun ce shirin SDGs na MDD zai bunkasa ci gaban Afrika
2015-09-25 12:12:39 cri

Wasu kwararru daga kasar Kenya sun ce, aiwatar da shirin ci gaba na SDGs wanda shugabannin manyan kasashen duniya suka bullo da shi yayin babban taron MDD a birnin New York, zai yi matukar habaka ci gaban tattalin arzikin kasashen Afrika.

Ana sa ran shugabannin kasashen duniya sama da 150 ne za su gudanar da taro daga ranar 25 zuwa 27 ga watan Satumba, domin tattaunawa kan daftarin shirin samar da ci gaba na shekarar 2015, shirin zai mai da hankali ne kan tunkarar wasu daga cikin kalubale dake damun al'ummar duniya, kamar su talauci da sauyin yanayi da samar da daidaito.

A hirarsu da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua, masanan sun ce, sabon shirin zai taimaka wajen tunkarar matsalolin dake hana ruwa gudu wajen ci gaba, musamman talauci da sauyin yanayi.

Kikaya, daya ne daga cikin masanan ya ce, wannan sabon shiri wanda ake sa ran shugabannin duniya za su amince da shi cikin wannan mako zai taikama wajen samar da ci gaba ta fuskar zamantakewar al'umma da muhalli, musamman ta hanyar shigar da wadanda matsalar ta fi shafa cikin aiwatar da shirin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China