in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fasahohin sadarwa sun taimaka wajen kyautata zaman rayuwar jama'a a kauyuka
2017-05-18 10:51:57 cri

Ranar 17 ga watan Mayu rana ce ta sadarwa ta duniya. A halin yanzu, bunkasuwar sadarwa, ta yi matukar tasiri ga zaman rayuwar dan Adam. A wasu kauyuka na kasar Sin, fasahohin sadarwa bisa tushen yanar gizo, sun taka muhimmiyar rawa wajen yaki da talauci, da kyautata zaman rayuwar jama'a.

A yankin iyaka dake tsakanin lardunan Shaanxi, da Gansu, da yankin Ningxia dake yammacin kasar Sin, bunkasuwar sha'anin sadarwa ta kawo babban canji ga zaman rayuwar jama'a.

A wata makarantar firamare dake kauyen Fenghuang na birnin Pingliang na lardin Gansu, yara suna kallon farin allo dake gaban aji, suna kuma karanta abun da ke jikin sa bisa jagorancin malami. Kauyen Fenghuang na yanki mafi talauci a Liupanshan dake yankin iyaka, a tsakanin lardunan Shaanxi, da Gansu da yankin Ningxia. Ba shi da ci gaban tattalin arziki ba, kana babu sha'anin ba da ilmi mai kyau.

Amma bayan samar da hidimar yanar gizo a yankin, an samu hanyoyin ba da ilmi masu kyau ga wannan kauye. Shugaban makarantar firamare ta kauyen Fenghuang Jing Fengxin ya bayyana cewa, sabbin hanyoyin ba da ilmi, da yin karatu, da ba a taba ganin irin su ba, sun haifar da kyakkyawar makoma ga yara dake karatu a wajen. Ya ce,

"Bayan da aka shigar da kananan wayoyin aikewa da sako cikin sauri tun a shekarar bara, an sa kaimi ga malamai da yara, wajen kara kwazo a aikin koyo da koyarwa. Alal misali, a yayin da suke yin kos na gwaji, za a kalli gwaji kai tsaye ta yanar gizo, yara suna nuna matukar sha'awa a wannan hanya."

Kamfanin China Telecom ya gudanar da aikin shigar da kananan wayoyi na aikewa da sako ta haske a kauyuka tun daga shekarar 2015 don sa kaimi ga bunkasa sha'anin yanar gizo a yankuna masu talauci. A shekarar 2016, ma'aikatar harkokin masana'antu da sadarwa, da ma'aikatar kudi ta kasar Sin sun hada gwiwa wajen gabatar da tsarin ba da rangwame kan hidimar sadarwa, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin ya ba da kudi yuan biliyan 8 da miliyan 700, don sa kaimi ga kamfanonin sadarwa su zuba jari, da kudi yuan biliyan 23, ta haka za a taimaka wajen ginawa da kyautata sha'anin yanar gizo a kauyuka dubu 100, ciki har da kauyuka masu talauci dubu 31.

Shugaba Jing ya bayyana cewa, kafin hakan an ajiye farin allo a kowane aji, amma yanar gizo ba ta da sauri sosai, don haka ba a iya yin amfani da allon yadda ya kamata. A halin yanzu, bayan da aka kyautata yanar gizo a kauyen, malamai na iya samun damar ba da ilmi irin na tsarin birane daga yanar gizo cikin sauki, ta haka yara dake kauyen suna iya koyon abubuwa kamar yadda yara dake birane suke yi.

Ban da sha'anin ba da ilmi, kyautata yanar gizo ya sa kaimi ga bunkasuwar ciniki ta yanar gizo a kauyuka. Bayan da aka shigar da yanar gizo mai sauri a kauyen Jiuji dake garin Shangliang, Jing Jianping da ya yi aiki a birnin Beijing ya koma garinsa, inda ya kafa kantin sayar da kaya na farko ta yanar gizo a kauyen. Jing Jianping ya bayyana cewa, ta wannan kanti, mazaunan kauyen na iya sayar da kayayyakin amfanin gona ta yanar gizo cikin araha da kuma sauri, kana za su iya sayen kayayyakin rayuwa masu araha ta yanar gizo. Jing Jianping ya bayyana cewa,

"Yawan kayayyakin amfanin gona da muke sayarwa ya kai 3064, yawan kudinsu ya kai yuan dubu 510. Ya zuwa watan Agusta na shekarar bara, mun taimakawa masu shuka tuffa guda 8, wajen sayar da tuffa da nauyinsu ya kai ton 12, yawan kudinsu ya kai yuan dubu 96."

Haka zalika kuma, yanar gizo mai sauri ta kawo sauki ga mazaunan birnin Pingliang, wajen ganin likitoci, da mayar da kudin da aka kashe domin ganin likitoci. Ta hanyar hidimar musamman ta kiwon lafiya ta yanar gizo, mazaunen kauyen suna iya ganin likitoci a karamin asibitin dake kauyen, daga baya za su iya samun kudin da suka kashe a wannan fanni a ofishin kauyen, ta haka ba su bukatar tafiya sauran wurare masu nisa, don yin hakan. Daraktan ofishin sadarwa na PingLiang Zhang Xiaogang ya bayyana cewa, moriya da bunkasuwar sha'anin sadarwa, ta ba su damar kara taimakawa jama'ar dake yankin. Ya ce,

"A mataki na gaba, za a gina yanar gizo mai sauri a sauran kauyuka 243. Burinmu shi ne shigar da yanar gizo mai sauri a gidajen mazaunen wurin su dubu 100 kafin karshen bana, da haka dukkan jama'a dake wurin za su iya amfani da irin wannan yanar gizo, wanda ta haka ne za a iya kara kawo moriya gare su." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China