Yawan ayyukan da kasashen Afirka suka jawo jari daga kasashen waje ya ragu da kashi 12.3 cikin dari a shekarar 2016
Bisa wani rahoto game da karfin jawo jari na nahiyar Afirka na shekarar 2017, wanda hukumar Ernst & Young ta gabatar a kwanakin baya, an ce, yawan ayyukan da kasashen Afirka suka jawo jarin su daga kasashen ketare kai tsaye a shekarar 2016 ya kai 676, adadin da ya ragu da kashi 12.3 cikin dari bisa na shekarar 2015, amma kuma yawan jarin da aka zuba ya karu da kashi 31.9 cikin dari.
Rahoton ya nuna cewa kasashen da suka fi jawo jari daga kasashen waje kai tsaye su ne Afirka ta Kudu, Morocco, Masar, Nijeriya da Kenya, kuma yawan ayyukan da aka jawo jari cikin su a kasashen biyar, ya kai kashi 58 cikin dari bisa na dukkan nahiyar Afirka. (Zainab)