A wani taron tattaunawa da aka gudanar a a birnin Durbana yayin taron tattaunawar harkokin tattalin arziki na Afirka, Kuseni Dlamini, shugaban kamfanin Massmart Holdings yace, makomar cigaban nahiyar Afrika ya ta'allaka ne da kasashe biyu mafiya karfin tattalin arziki a nahiyar, kuma sun kasance a matsayin ginshikai wajen magance kalubalen da al'umma ke fuskanta a nahiyar.
Dlamini yace Najeriya da Afrika ta kudu gaba daya suna bada gudumowar kashi 60 cikin 100 na karfin tattalin arzikin GDP na kasashen Afrika da ke kudu da hamadar saharar, kuma Afrika ba zata iya cimma nasara ba matukar wadannan kasashen biyu basu samu nasara ba.
Geoffrey Qhena, babban jami'in kamfanin Industrial Development Corporation wato (IDC) na kasar Afrika ta kudu, ya bayyana cewa manyan kasashen biyu bai kamata su dogara wajen shigo da kayayyaki daga waje ba, sai dai a cewarsa kamata yayi su kakkafa masana'antu da kamfanoni domin amfanin kansu da sauran kasashen dake nahiyar. Yace ya kamata shugabannin su yi watsi da duk wasu bambance bambance dake tsakaninsu su hada kai wajen samar da muhimman abubuwan da zasu kawo cigaban nahiyar.