A wani bangare na taron cibiyar inganta noman masara da alkama ta duniya, Daraktan shirin noman masara na cibiyar, Boddupali Prassana, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, gwamnatocin nahiyar Afrika ba su da wata mafita, illa su sake sauya inda suka sa gaba, domin tunkarar manufar Washington na rage kudin da take bayarwa ga gudanar da harkokin nahiyar.
A baya-bayan nan ne shugaba Donald Trump, ya sanar da rage yawan kudaden da ake warewa hukumar raya kasashe ta Amurka wato USAID.
Idan aka aiwatar da wannan sabon tsarin, ana sa ran zai yi mummunan tasiri ga kasashe masu tasowa, la'akari da yadda hukumar ke taimakawa shirye-shiryen samar da ci gaba a kasashen Afrika 30.
Sai dai, umarnin ba zai shafi kudaden da ake warewa na yaki da cutar kanjamau ba, amma kuma, zai shafi shirye-shiryen tallafawa bincike a fannonin harkokin noma da sauyin yanayi a yankin kudu da hamadar Sahara. (Fa'iza Musatpha)