Waiganjo, ta lashe kyautar a karon farko bayan ta yi nasarar doke wasu matan 4 da suka fafata inda ta samu lambar yabon, a matsayin matashiyar ta yi nasarar a fannin kimiyya.
Bikin na Miss Geek Africa ana shirya shi ne da nufin zaburar da yan mata na nahiyar Afrika a matsayin wata hanyar magance matsalolin da suka shafi matan na Afrika.
Tun a shekarar 2014, gasar ta janyo hankalin mata matasa a fannin fasahar sadarwa don neman mafita a kasar Rwanda.
Amma a wannan shekarar, gasar yan matan a fannin na ICT, masu shirya gasar, sun fadada shirin a tsakanin mambobin kasashen Afrika 17, sun kuma amince cewa za'a bada lamabar yabon ne ga wadda ta zo ta farko a gasar ta Miss Geek Africa, da hadin gwiwar Smart Africa.
Wadannan mata sun kuma nuna hazaka inda suke yunkurin ganin matan sun kasance a sahun gaba wajen warware matsaloli a fannonin kimiyya, fasaha, fasahar kere kere, da lissafi.
Yan matan ICT na Rwanda, wata kungiya ce ta kwararrun mata wato STEM, wadanda suka kasance abin koyi ga sauran yan mata na Rwandan a fannonin STEM.
Matashiyar data zo ta farko ta jaddada aniyar cigaba da yin fafutuka wajen amfani da ICT a matsayin wata hanyar samar da cigaban mata da samar da daidaito.(Ahmad)