Kasashen Morocco da Nijeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar aikin shimfida wani muhimmin bututun gas da zai hada kasashen yammacin Afrika a jiya Litinin.
A watan Disamban bara, lokacin da sarki Mohammed na shida na Morocco ya kai ziyara Nijeriya ne aka cimma yarjejeniyar aikin shimfida bututun iskar gas din da aka yi wa lakabi da The Gazoduc, wanda zai ratsa ta kasashen yammacin Afrika, kuma mai yuwa ya dangana zuwa Turai.
Da yake gabatar da aikin, ministan harkokin wajen Morocco Nasser Bourita ya ce, shimfida bututun zai yi kyakkyawan tasiri kan mutane sama da miliyan 300, domin zai samar da wani yanayi na gasa wajen samar da wutar lantarki a yammacin Afrika.
A nasa bangaren, ministan harkokin wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama ya jadadda cewa, kammala cimma yarjejeniyar alama ce dake nuna nasarar dangantaka dake tsakanin Rabat da Abuja.
Har ila yau a jiyan, kasashen sun rattaba hannu kan yarjejeniyar inganta samar da taki a Nijeriya. Yarjejeniya na da nufin lalubowa tare da daukaka darajar ma'adanar sinadarin phosphate a Nijeriya, ta yadda kasar dake yammacin Afrika za ta fadada aikin sarrafa taki.(Fa'iza Mustapha)