Wata hukumar MDD ta bukaci Najeriya da ta nemi goyon bayan kasashen duniya don mara mata baya a yakin da take yi da rashawa.
Ofishin MDD mai yaki da muggan laifuka da ta'ammali da haramtattun kwayoyi (UNODC) dake Abuja ya bayyana cewa, ko da yake Najeriya ta yi nisa matuka a shirinta na yaki da rashawa, amma dole ne kasar ta yi la'akari da cewa, yaki da rashawa yana bukatar yin aiki tukuru, kuma ba aiki ne da za'a iya kammala shi cikin wuni guda ba.
Jennifer Bradford, jami'ar sashen shari'a ta hukumar UNODC, ta ce yaki da rashawar yana bukatar yin hadin gwiwa a cikin gida har ma da kasa da kasa saboda a cewarta babu kasar da za ta iya yakar rashawa ita kadai.
Jami'ar MDD ta kara da cewa, jajurcewa da yin aiki tukuru su ne kadai za su taimaka wajen samun nasarar shirin yaki da rashawa.
Ministan shari'a na Najeriya Abubakar Malami ya bayyana cewa, gwamnati tana daukar dukkan matakan da suka dace wajen yaki da rashawa domin samar da tsabta a dukkan fannoni.(Ahmad Fagam)