An fara kafa kamarorin sa ido da aka fi sani da CCTV Camera guda 300 a fadin jihar Lagos dake kudu maso yammacin Nijeriya, wadda kuma ke a matsayin cibiyar tattalin arzikin kasar a jiya Litinin.
Kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Olufemi Odubiyi ya ce, an samu jinkirin kafa kamarorin ne saboda yanayin rashin tabbas da kasuwar musayar kudaden ketare ke fuskanta.
A watan Agustan 2016 ne, gwamnatin jihar ta ce za ta fara kafa kamarorin sa ido guda 13,000 a cikin watan Satumban da ya gabata.
Olufemi Odubiyi ya yi bayanin cewa, an samu jinkirin fara gudanar da aikin ne saboda yanayin da kasuwar musayar kudaden ketare ke ciki.
Ya ce, an kammala tsara yadda za a gudanar da aikin cikin matakai, kuma a matakin farko, an riga an tura kayayyakin aikin da ake bukata na kafa kamarori 300 da aka fara kai wa jihar daga ketare.
A cewar kwamishinan, kamarorin na CCTV za su inganta tsaro tare da kare aukuwar laifuka. (Fa'iza Mustapha)