in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Morocco ce kasar Afrika ta farko da za ta samu jirgin kasa mai saurin tafiya nan da 2018
2017-04-20 13:07:58 cri

Kasar Morocco za ta zama kasar Afrika ta farko da za ta mallaki jirgin kasa mai saurin tafiya nan da shekar 2018.

Babban daraktan hukumar kula da zirga-zirgar jirgin kasa ta kasar ONCF, Mohamed Rabie Khlie, ya fada a lokacin taron kasa da kasa da aka gudana domin tattauna kan batun game da tsaron zirga-zirgar jirgin kasa a arewacin birnin Tangier cewa, a yanzu haka aikin gina jirgin mai saurin tafiya TGV, ya kai kashi 86 bisa 100. Jami'in na kasar ta Morocco ya ce, kasar ta ninka kudaden zuba jari a a fannin gina layin jirgin kasar mai saurin tafiyar cikin shekaru 10 da suka gabata, wanda ya kai dalar Amurka biliyan 3.4 tsakanin shekarun 2010 da 2015.

Tun a farkon wannan shekara ne, aka yi gwajin jirgin na French-made double-decker TGVs, tun gabanin kaddamar da shi, wanda ya hada da birnin Tangier na tekun Mediterranean da Casablanca, babban birnin kasuwan kasar ta Morocco.

Sabon jirgin, wanda zai iya gudun mil 200 cikin kowace sa'a, zai rage lokacin zirga zirgarsa a tsakanin birane biyu daga karfe 5 zuwa karfe 2.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China