in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban gidan talabijin Morocco ya fara watsa wani shirin Sinanci
2017-04-21 09:44:46 cri

Babban gidan talabijin na kasar Morocco 2M, ya fara watsa wani shirin drama na Sinanci da aka fassara zuwa harshen Larabci.

A jiya Alhamis ne aka yi bikin kaddamar da shirin mai suna "A Happy Life" karkashin jagorancin shugaban sashen yada labarai na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Liu Qibao, da kuma sakatare janar na ma'aikatar yada labarai da al'adu ta kasar Morocco Mohammad Ghazali.

Yayin bikin, shugaban gidan rediyon kasar Sin CRI, Wang Gengnian da takwaransa na gidan talabijin na 2M Salim el Sheikh, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar watsa shirye-shiryen drama na kasar Sin a tashar ta Morocco.

Wang ya ce, an kulla yarjejeniyar ce da nufin kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kafafen yada labarai na kasar Sin da Morocco, ya na mai cewa, hadin gwiwar na kunshe cikin kawancen dake tsakanin kasar Sin da kasashen nahiyar Afrika, da kuma ziyarar da jami'an watsa labarai na kasashen biyu ke kai wa juna.

Ya jaddada cewa, CRI ta kulla daddadiyar dangantaka mai karfi da kafafen yada labaran Afrika da dama, inda ya ce, cikin shekaru da dama da suka shude, wadanan kafafen yada labarai sun yi ta watsa shirye-shiryen Sinanci da dama cikin harsunan su, ya na mai cewa, shirye-shiryen sun samu karbuwa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China