Rahotanni na cewa, wani jami'in hukumar WHO dake kula da harkokin Afirka, ya riga ya isa birnin Kinshasa, kuma tawagar kwararru ta WHO na fatan isa kasar cikin sa'o'i 48, don tattaunawa tare da mahukuntan Kongo Kinshasa, da wasu hukumomin kiwon lafiyar kasar, da nufin neman hanyoyi mafiya dacewa don magance yaduwar cutar.
A shekarar 2014 ne wannan cuta ta Ebola ta bulla a wasu kasashen yammacin Afirka, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane sama da dubu 11, ciki kuwa hadda wasu mutane 66 da suka kamu da cutar a kasar ta Kongo Kinshasa, kuma a lokacin mutane 49 sun rasa rayukansu. (Bilkisu)