Sakamakon wasu sabbin bincike na kimiyya, ya nuna cewa, kwayoyin cutar Ebola sun sauya daga yanayin da aka san su a shekaru da dama, inda suka rikide zuwa wani nau'i mai saurin yaduwa a tsakanin mutuna, yayin annobar cutar da ta barke tsakanin shekarun 2013 zuwa 2016.
Sauyin da kwayoyin cutar suka yi, shi ne musabbabin kisan mutane sama da 11,000 da cutar ta yi a sassan duniya da dama, kamar dai yadda sakamakon binciken da wasu gungun masana, na cibiyoyin kasar Amurka guda biyu suka bayyana.
Sakamakon binciken wanda aka buga a mujallar kimiyya ta "US Journal Cell", ya nuna cewa, a baya kwayoyin cutar ba su da karfi na tsallakawa zuwa jinshin mutane daga jikin dabbobin dake dauke da su, sabanin yanayin da aka gani na saurin yaduwar cutar cikin 'yan shekarun nan.(Saminu)