Da yake magana a wata hira da kamfanin dallancin labarai na Xinhua, shugaban Saliyo ya nuna cewa yana jiran kuma ga wani karin zurfafa dangantaka tare da Sin a nan gaba.
Shugaban yace yana tune da zuwan jirgin sama cike da ma'aikatan kiwon lafiya da kayayyaki na kasar Sin jim kadan bayan barkewar cutar Ebola, wani mataki wanda a cewarsa ya bada kwarin gwiwa ga tallafin kasa da kasa a cikin yaki da cutar Ebola.
Kasar Sin ta samar da dukkan abubuwan da aka bukata ta fuskar ma'aikatan kiwon lafiya da magunguna da kuma magungunan ajiya, in ji mista Koroma, kafin ya kara da cewa tallafin Sin bai tsaya nan a huldar dangantaka ba, har ma kuma a bangarori daban daban ta hanyar bankin duniya, hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO) da kuma sauran hukumomin MDD.
Ya kuma fifita huldar dangantaka dake tsakanin Saliyo da Sin dake bisa tushen abokantaka da yarda da juna, tare da jaddada cewa Sin abokiya ce ta kwarai.
Haka kuma ya bayyana wasu sauran taimakon Sin da dama ga cigaban ababen more rayuwar jama'a a kasar, da kuma bangarorin noma, kiwon lafiya da ilimi. Yanzu ganin cewa Sin ta zama babbar kasa mai karfi a duniya, yana da kyau ga kasar Saliyo da ta yi koyi da kwarewar kasar Sin in ji shugaban Koroma, tare da jaddada cewa zai yi nazari a yayin ziyararsa a kasar da hanyar cigaban tattalin arziki da kasar Sin ta dauka haka kuma yadda aka kafa yankunan tattalin arziki da suka taimaka sosai wajen yawaita hanyoyin tattalin arzikin kasar Sin. (Maman Ada)