An dai yi gwajin allurar ne a kasar Guinea a shekarar 2015, kan mutane 11,841, kuma cikin mutane 5,837 da aka yiwa riga kafin, babu wanda ya kamu da cutar cikin kwanaki 10 ko fiye. Kana an samu kamuwar mutane 23 cikin kwanaki 10 a bangaren wadanda ba a yi musu allurar ta riga kafi ba.
Wata mujallar likitanci mai suna Lancet ce ta tabbatar da rahoton binciken wannan allurar mai suna rVSV-ZEBOV.