in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 16 suka jikkata a sakamakon fashewar wani abu a dab da wata cibiyar horas da 'yan Sanda a Masar
2017-04-02 14:16:40 cri
A labarin da kamfanin dillancin labarai na MENA ya bayar, ya ce a kalla 'yan sanda 14 tare da fararen hula biyu ne suka jikkata a jiya Asabar a wata cibiyar horar da 'yan sanda da ke lardin Delta dake arewa maso yammacin birnin Alkahira.

Tuni dai aka garzaya da mutanen da suka jikkatan zuwa wani asibiti dake kusa don yi musu magani, a yayin da aka kuma tsaurara matakan tsaro tare da killace wajen da harin ya afku, kuma motocin daukar marasa lafiya sun isa wurin cikin gaggawa.

Kasar Masar dai ta sha fama da hare-haren ta'addanci da suka hallaka daruruwan 'yan sanda da sojoji tun bayan da sojojin suka hambarar da tsohon shugaban kasar Mohamed Morsi a watan Yulin shekarar 2013.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China