Amurka za ta turo wakilai a taron shawarar "ziri daya da hanya daya" da za a bude a birnin Beijing
Mataimakin ministan kudi na kasar Sin Zhu Guangyao ya shaidawa taron manema labarai a yau Jumma'a cewa, Amurka za ta turo wakilai a dandalin hadin gwiwar kasa da kasa game da shawarar "Ziri daya da hanya daya".
Taron dandalin da aka shirya gudanarwa daga ranar 14-15 ga wannan wata a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, shi ne babban taron kasa da kasa game da shawarar "Ziri daya da hanya daya" tun lokacin da kasar Sin ta gabatar da wannan shawara a shekarar 2013. (Ibrahim Yaya)