Babban jami'in ma'aikatar kasuwancin na kasar Sin Qian Keming ya bayyana cewa, shawarar "Ziri daya da hanya daya" ta sa sabon kaimi ga ci gaban kasashen dake halartar shawarar, da kuma dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda.
Wannan shawarar ta zo ne a daidai lokacin da tattalin arzikin duniya ke fuskanta matsaloli, kuma tuni tattalin arzikin wasu kasashen duniya ke fama da koma baya, mataimakin ministan kasuwancin Sin Qian Keming ya tabbatar da hakan a taron manema labarai..
Ya ce, kasashen duniya da dama dake karkashin shawarar "Ziri daya da hanya daya" sun amfana a zagayen karshe na shirin dunkulewar tattalin arzikin, kuma shawarar za ta ba su damammaki wajen samun bunkasuwar tattali arziki da samun ci gaba, kana dunkulewar ta kara samar da mu'amala da kuma daidaito ga kasashen.
Qian ya ce, yana ganin yiwuwar samun damammaki na bunkasuwar kasuwanci da zuba jari ga kasashen dake karkashin shawarar sakamakon yadda tattalin arziki da albarkatun da suke da su yake kara samun tagomashi.
Shawarar wadda aka kaddamar da ita a shekarar 2013, da nufin yin cudanya a harkokin ciniki da samar da kayayyakin more rayuwa wadda ta hade nahiyoyin Asiya da Turai da Africa, ta haifar da ci gaba. Sama da dala biliyan 50 kasar Sin ta zuba jarinta a kasashen dake karkashin shawarar. Kasar Sin tana mu'amalar kasuwanci da kasashen wanda ya tasamma RMB yuan tirilan 20 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 2.9 tsakanin shekarar 2014-2016, in ji Qian.(Ahmad Fagam)